Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Kannywood:Yadda Nafisa Abdullahi tayi kaca-kaca da Rahma Sadau


Labarun da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni da cewa da alamu takun sakar da ke a tsakanin manyan jarumai mata a masana'antar Kannywood watau Rahma Sadau da Nafisa Abdullahi na shirin daukar sabon salo. Majiyar tamu dai ta ruwaito cewa a cikin wata fira da tayi, Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa ita a wurin ta Rahma Sadau ba kowa bace don haka kuwa ba ta isa tayi gasa da ita ba. NAIJ.com dai a wani bincike da tayi ta gano cewa rashin jituwar dake a tsakanin jaruman biyu ya samo asali ne a wattanin baya tun lokacin da za'a fara shirin fim din Rariya na Rahma Sadau din da aka ce ta gayyaci Nafisa Abdullahi amma taki yadda tayi bayan kuma ta karbar mata makudan kudade. Binciken namu kuma ya bayyana cewa hakan ne ma ya sanya jarumar Rahma Sadau ta maka Nafisa Kotu domin a bi mata hakkin ta inda daga nan kowa ya ja daga cikin su yana zafafan kalamai ga yar uwar ta. -naij

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies