Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Kalli rawar da wata fitacciyar jarumar Fina finan Hausa ta taka a wani ƙasataccen fim na Turanci (Hotuna)Shahararriyar jarumar fina finan Kannywood, Maryam Booth ta fito cikin wani sabon shirin Fim na Turanci, mai suna ‘Sons of the Caliphate’, Yayan Sarauta.
Majiyarmu ta ruwaito, wannan Fim na nuni ne ga rayuwar wasu matasa yan gida daya dake gogoriyon neman mulki, ramuwar gayya da kuma so da kauna, sune Kalifah, Nuhu da Dikko.
Maryam Booth ta fito ne a matsayin yar maye, wato mai shaye shaye, da nufin fadakarwa a kan illolin shaye shaye ga mai yinsa, kamar yadda Hausazone.com ta ruwaito.
Daga cikin jaruman Kannywood da suka taka muhimmin rawa a cikin wannan Fim, akwai Maryam Booth, Rahama Sadau da kuma Yakubu Muhammed, sa’annan ana nuna wanna shiri ne a duk sati a Ebony Tv.
A wani labarin kuma, afuwar da hukumar tace fina finan Hausa ta yi ma jaruma Rahama Sadau ya bar baya da kura, inda kungiyar yan Fim na Kannywood ta yi watsi da afuwar.
Shugaban kungiyar, Kabiru Maikaba ne ya sanar da haka a ranar Alhamis 11 ga watan Janairu, inda yace har yanzu kungiyarsa bata yafe ma Rahama Sadau ba.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies