Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Masifar Dake Kannywood Ta Wuce Misali - Inji Adam A ZangoMasifar Dake Kannywood Ta Wuce Misali - Inji Adam A Zango
Ni ba 'dan daudu bane kuma ni ba 'dan maula bane. Sannan ni ba mushiriki bane, bani da malami ko matsafi. Da Allah ka'dai na dogara.
Idan kuma akwai malamin da yace na taba wajansa ko kuma wanda ya taba bani kudi kyauta ba tare da nayi masa aikin komai ba to dan girman Allah kada ya rufa min asiri, tun daga kan 'yan siyasa, sarakuna, gwabnati, ko masu kudi ko 'yan mata. Duk abinda na mallaka arayuwata guminane ya bani ba dan adam ba.
Motar hawa gida ko fili. Dan haka ba wanda ya isa yasa ni inyi abinda banyi niyya ba tunda ba wanda ya taya ni kare mutuncin kare daukaka ta ba. .
Dan haka hanya daya zaku iya dakatar da daukaka ta, hanyar itace ku da katar da numfashina. Sai dai kuma kash hakan ba'a hannun ku yake ba. Ku ta yawo da ni kuna bata min suna dan Allah ya fifita ni akan ku. .
Kunce min arne kunce min gay ('dan luwa'di) kunce min mai girman kai, amma duk da haka masoyana ba wanda ya guje ni basu daina sayan fina finai da wakokina ba.
"Haba dan Allah mai nayi muku duk wanda na taimaka arayuwata sai ya dawo yana yakata". To nakai bango Billahillazi La'ilaha'illahu duk wanda ya kara taba ni sai na tona masa asiri.
. Sannan duk wanda ya rufa min asiri akan abubuwan dana lissafa Allah ya tona masa nasa. Ban kira sunanan kowa ba a yanzu amma next time zan kira sunan kowaye idan ya kara bata min suna. Ina da 'yaya' ya zama dole na fara kare mutuncin kaina da martabana kafin ya yi affecting din su don Allah kadai yasan gawar fari. Sannan zanja tunga ga makiyana na kannywood dan hakane kadai za'a banbance tsakanin aya da tsakuwa.
Masoyana ku gafarce ni akan abubuwan dana fada an kure ni ne.
Yanda a ko ina ake samun nagari da bata gari hakazalika acikin kannywood akwai nagari da bata gari, kuma wallahi billahi daga yau ba za'a kuma yi min kazafi nayi shuru ba dan kowa acikin yasan kowa. Shi yasa idan akace mana jahilai bana damuwa domin nima nagano hakan. Tunda ance amfanin ilmi aiki da shi. .
Masifar da masana'antar kannywood take ciki ya wuce misali, sabida zalinci, fasikanci, riya, eye service (sa'ido) da kuma cin amana da ake aikatawa karara amma daga anyi magana sai ace matan cikin mu ke jawo mana. Wlh matan mu basu da laifi domin addini bai taba ba mace damar zama ba mai kula da ita ba. Amma a kannywood fim mace daya ko yaro zasu yi sai kaga sun bude kamfanin kansu harma su dinga daukar sababbin 'yan wasa.
Babu tone tone domin da dama sun san kansu.
Dan haka mu daina jin haushin maganar da wasu suke yi mana mu karba laifin mu gyara wata kila nan gaba kadan ayi alfahari da mu.
Duk abinda na rubuta idan akwai karya wani ya fito ya karya ta ni ko kuma a kore ni.
Duk wadda tace sai na neme ta kafin in sata a fim ta fito gidan television ko radio station ta fadawa duniya.
Idan kuma ta rufa min asiri Allah ya to nata asirin.
Rubutawa: Mujallar Fim

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies