Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Yadda Wani Mutum Ya Yi Wa Abokiyar Aikin Shi Fyade Bayan Ya Barbada Wiwi A Abincin TaWani mutum da ke aikin kamfani a jahar Lagos mai suna Victory Eno ya gamu da fushin hukuma bayan da ya sanyawa wata abokiyar aikin shi wiwi a abinci sannan ya yi amfani da damar wajen yi mata fyade.
An gurfanar da mutumin a kotun majistare da ke Ikeja a jiya Litinin.
Lauyan mai kara, Benson Emurhi ya fadawa kotun cewa Eno ya aikata laifin ne a ranar 24 ga watan Disamba, bayan da ya baiwa abokiyar aikin na shi mai shekaru 22 shinkafar da ya riga ya zuba wiwi a ciki.
Ya ce bayan ta ci shinkafar ne sai ta fara jin jiri, inda shi kuma ya yi amfani da damar wajen yi mata fyade.
Laifin fyade wanda ya saba da da sashe na 261 na dokar jahar Lagos dai ya na da hukuncin daurin rai da rai a jahar.
Toh sai dai Eno bai amsa laifin na shi ba. Alkalin kotun Bolanle Osunsanmi ta bayarda belin shi akan Naira dubu dari uku tare da bukatar masu tsaya masa.
Ta daga sauraran karar zuwa ranar 16 ga watan Afrilu.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies