Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Dalilin Da Ya Hana Ni Sake Yin Aure – Samira Ahmad


Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood mai suna Samira Ahmad ta fito ta bayyana babban dalilin da ya sa har yanzu ba ta sake yin aure ba.

Jarumar da ke zaman tsohuwar matar shahararren mawakin nan kuma mai shirya fina-finai watau T. Y Shaba ta bayyana cewa yanzu haka miji nagari take nema domin ta sake yin aure.

Tsohuwar jarumar a baya sun yi aure da jarumin fim din inda Allah ya albarkace su da samun diya mace a tsakanin su kafin zaman na su ya zo karshe.

‘Yan fim dai da dama na shan suka wajen jama’a musamman ma akan maganar aure inda ake alakanta su da cewa ba su son zaman aure ko kadan, zargin da su kuma jaruman sukan karyatawa a ko da yaushe.

Jarumar ta yi addu’ar Allah ya ba ta miji na gari a dandalin sada zumunta, kuma jama’a da dama sun tayata da cewa Amin.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies