Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Dandalin Kannywood: Ko na yi aure zan cigaba da harkar fim - Hannatu BashirJarumar dai ta kuma ayyana cewa kawo yanzu ita ba ta da wata sana'ar da take yi wadda ta wuce harkar fim

- Jarumar ta bayyana cewa kawo yanzu ta fito a cikin fina-finai akalla 50 a tsawon shekaru 7

Daga daga cikin fitattun fuskoki a fafajiyar masana'antar shirya-fina-finan Hausa ta Kannywood mai suna Hannatu Bashir ta fito ta bayyana cewa ita fa ko da ta yi aure to tabbas zata cigaba da harkokin ta na fim musamman ma bangaren shiryawa da sauran ayyukan bayan fage.Fitacciyar jarumar dai ta kuma ayyana cewa kawo yanzu ita ba ta da wata sana'ar da take yi wadda ta wuce harkar fim din sannan kuma a shirye take ta bar fitowa a cikin fina-finai watau 'aktin' za zarar ta samu miji ta kuma yi aure.

Majiyarmu  ta samu haka zalika cewa jarumar ta yi karin haske game da batun da ake na cewa mafi yawancin 'yan matan da ke yi harkar fim 'yan iska ne inda ta bayyana cewa sam ba haka bane domin kuwa da yawa daga cikin wadanda ake kamawar ba 'yan fim din ne ba.

Da karshe ne kuma sai jarumar ta bayyana cewa kawo yanzu ta fito a cikin fina-finai akalla 50 a tsawon shekaru 7 da ta shafe tana harkar kuma fim fin 'Kotun Ibro' shine fim din ta na farko.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies