Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Dandalin Kannywood: Mazajen aure muke nema - inji Gimbiya da Sa'adatu na Dadin Kowa
Mazajen aure muke nema - inji Gimbiya da Sa'adatu na Dadin Kowa

- Sun ce rawar da suke takawa a cikin wasan Dadin Kowa yayi kusa da irin rayuwar su ta gaske

- Sun yi jinjina tare da godiya da dumbin masoyan su a duk inda suke a fadin duniya
Fitattun fuskokin nan na wasan kwaikwayon Dadin Kowa da ake haskawa a tashar tauraron dan adam ta Arewa 24 kuma daya daga cikin 'yan biyun masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood watau Gimbiya da kuma Sa'adatu sun bayyana cewa suna addu'ar Allah ya kawo masu mijin aure suma.

Su dai jaruman sun bayyana cewa kamar sauran mata, suma suna addu'a Allah ya kawo masu miji mai nagarta domin su samu su yi aure domin acewar su cikar darajar mace a dakin mijin ta. Sai dai muna burin mu yi aure tare, hakan ne ma ya kawo jinkirin auren, domin da a ce daban-daban za mu yi da tuni mun yi.

Majiyarmu  haka zalika ta samu dai cewa jaruman kuma sun bayyana cewa irin rawar da suke takawa a cikin wasan kwaikwayon Dadin Kowa yayi kusa da irin rayuwar su ta gaske.

Daga karshe kuma jaruman sun bayyana cewa a shirye su ke su ajiye sana'ar fim gaba daya indai har za suyi aure.

Haka nan kuma jaruman sun yi jinjina tare da godiya da dumbin masoyan su a duk inda suke a fadin duniya.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies