Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Dandalin Kannywood: Abunda na sa gaba bayan daina fitowa a fim – Sadiya Gyale -,,Shahararriyar jarumar nan ta Kannywood wacce aka dama da ita a lokutan baya, Sadiya Muhammad Gyale ta yi tsokaci akan abunda ta sa a gaba bayan barinta masana’antar ta shirya fina-finai.
A cewar jarumar ta kama sana’a ne gadan-gadan, inda ta ke saida kayayyaki daban-daban.
Sadiya tace tana saida kayan mata, na maza dama kayan noma domin tafiyar da al’amuranta na yau da kullun.

Jarumar ta bayyana hakan ne a wani hira da tayi da jaridar Leadership Hausa.

Da aka tambayeta kan batun aure, kyakyawar jarumar tace Insha Allah suna ta addu’a, Allah Ya kawo miji nagari mafi alheri.
A baya Majiyarmu ta kawo cewa tsohon mijin shahararriyar jarumar nan ta Kannywood, Sadiya Gyale wato Alhaji Abubakar Muhammad ya amsa kiran mahallicin sa.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies