Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Dandalin Kannywood: Jaruma Umma Shehu tayi tsokaci game da firar ta da Aminu MomoShahararriyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Umma Shehu a karon farko ta fito tayi tsokaci game da firar da tayi da fitaccen dan fim din nan, ma'aikacin tashar tauraron dan adam ta Arewa24, watau Aminu Sharif Momo a watannin baya.

Jarumar dai ta bayyana cewa ita ba ta ji haushi ba ko kadan bisa ga tambayar da yayi mata a wani shirin Kundin Kannywood game da lamarin addini domin a cewar ta suna fira ne ita kan nishadantarwa.

"Duk wanda ya kalli wannan firar ya san wasa ne da dariya a cikin sa" a cewar ta.

Majiyarmu  ta samu cewa kuma jarumar ta ayyana cewa ita bata da kawa a cikin masu shirya fina-finan don kuwa a cewar ta ba ta son dukkan wani abun da zai zo ya bata mata rai.
Da aka tambaye ta ko wani irin kalubale ne ta ke fuskanta a sana'ar ta ta sai jarumar ta ce ita tun da ta shiga harkar ba ta fuskantar kalubale sai dai alheri tun da ta shiga.

Naij hausa

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies