Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Jam'iyyar PDP ta baiwa Ummi Zeezee babban mukamiRahotanni sun kawo cewa babban jam’iyyar adawan Najeriya, PDP ta baiwa tsohuwar jarumar fina-finan Hausa na Kannywood, Ummi Zeezee babban mukami.

An bata mukamin shugabar riko ta mata ta kungiyar dake yiwa PDP kamfe gida-gida ta kasa baki daya.

Ummi da take bayyana hakan a shafinta na sada zumunta da muhawara tace ta godewa Allah da wannan mukami da ta samu yau, kuma tana fatan Allah ya baiwa jam'iyyar ta PDP mulki a zaben shekarar 2019.


Ummi dai tayi suna wajan caccakar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Hakazalika shugaban kungiyar yiwa PDP kamfen gida-gida na kasa, Ibrahim Dahiru Danfulani ya tabbatar da wannan mukami na Ummi Zeezee a jiya Juma'a.

Naij hausa

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies