Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Kura-Kuran Da Mata Ke Tafkawa Wajen Yin Kwalliyar Fuska
Akwai wasu kura-kuran da mata ke tafkawa wajen yin kwalliyar fuska wanda hakan ke iya janyo musu wasu matsaloli da kan iya zama barazana ga lafiyar fuskarsu.

1) Daya daga cikin kuskuren da mace ke yi idan ta yi kwalliyar fuska shine kwantawa barci ba tare da wanke fuska ba; lallai da kwai gajiya da kulawa da irin wadannan matsalar, amma sai mutum ya dage sosai. Datti da kuma maikon fuska na haifar da fesowar kuraje daga fuska. Don haka sai a kiyaye, A rika wanke fuska kullum kafin a kwanta barci.

2) Wani kuskuren shine rashin wanke kayan kwalliyar kamar su soson hoda da na gira da sauran su. Idan ba a wanke su, dauda za ta zauna a ciki. Ta yaya kuma za a sanya wa fuskar da aka wanke datti. Sai a kula domin yin hakan na haifar da cututtukan fuska.

3) Rashin shafa mai a fuska kafin a yi kwalliya, Ya kamata a dage da shafa mai a fuska kafin a yi kwalliya saboda yin hakan na rage shekarun mace, yana kuma sa kwalliya ta zauna da kyau a fuska.

4) Idan mace ta kasance mai yawan sanya kayan kwalliya a fuska, ya kamata ta rika wanke fuska akalla sau biyu a rana don hana wasu kurajen sakamakon dadewar kwalliyar.

5) Yin dilke na da matukar muhimmanci a jiki, domin yana karawa fuskar haske da kuma sheki.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies