Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Dandalin Kannywood: Ali Nuhu zai sake shirya Fim din Mujadala don tunawa da Ahmad S NuhuZuwa yanzu a iya cewa shirye shirye sun nisa matuka game da sabunta shirin shahararren Fim din nan da yayi suna a shekarun baya, watau Mujadala, sai dai abinda ya ja hankali yan kallo shi ne wanda zai maye gurbin marigayi Ahmad S nuhu.

BBC Hausa ta ruwaito Kamfanin shirya Fina finai na Mai Shadda ne zai dauki nauyin shirya wannan Fim, inda tace a ranar 10 ga watan Mayu ne zata fara nadirsa, haka zalika kamfanin ta bayyana cewar jarumi Umar M Shareef ne zai maye gurbin Ahmad.


Shi dai wannan Fim ya shahara a tsakanin yan kallo da masu bibiyan fina finan Kannywood, wanda ya kunshi taurari kamarsu Ali Nuhu, Sani mai Iska, Fati Muhammad, Abida Muhammad, Maijidda Abdulkadir da kuma Ahmad S Nuhu, wanda shine ya fitaccen jarumi a Fim din.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Ahmad ya rasu ne a shekarar 2007 sakamakon hadari da ya rutsa da shi a kan hanyarsa ta zuwa Maiduguri bayan fitowarsa daga garin Azare na jihar Bauchi inda ya gudanar da wasan Sallah.

A zamaninsa, Ahmad ya kasance jarumi mai tashe, domin kuwa tararuwarsa na haskawa, kuma yana da farin jinni a wajen yan kallo, gas hi mutum mai dadin hulda kamar yadda abokansa da na kusa suka tabbata

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies