Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Dandalin Kannywood: Ban mutu ba ina nan da raina - Sani ModaA yayin zantawar da manema labarai suka yi da shahararren jarumin finafinan Hausan nan Idris Sani Moda ta waya, ya karyarta jita-jitar da ake ta yadawa a kafafen yada labarai na zamani cewar ya rasu a daren jiya Litinin

A yayin zantawar da manema labarai suka yi da shahararren jarumin finafinan Hausan nan Idris Sani Moda ta waya, ya karyarta jita-jitar da ake ta yadawa a kafafen yada labarai na zamani cewar ya rasu a daren jiya Litinin.


Sani Moda ya kara da cewa ya yi mamakin yadda labarin mutuwar tasa ta yadu, wanda a dalilin hakan yake ta faman shan kira daga ciki da wajen kasar nan daga wurin masoyan sa, domin tabbatar da gaskiyar al'amarin. A cewar shi, an sami kuskuren sanarwar ne daga asibitin da yake kwance, inda suka bayyana shine a matsayin wanda ya rasu, ya bayyana cewar bashi Allah ya amshi rayuwar tasa ba na kusa dashi ne ya amsa kiran Allah. Sannan kuma ya bayyana cewar yana cigaba da samun lafiya.
A jiya ne dai kafafen yada labarai suka dinga yada cewar Allah yayi wa fitaccen jarumin rasuwa, bayan ya jima yana fama da jinya. 
Muna masa adu'ar Allah ya bashi lafiya mai inganchi yasa kuma hakan ya zama kaffara ce a gare shi.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies