Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Lafiya Uwar Jiki: Illar Yawan Amfani Da Magungunan Jima’i
A wani hira da kafafen yada labarai ta murya Amirka (VOA) ta yi da Dr. Mohammed Ladan wanda yake yawan tattaunawa da Sashen VOA ta Hausa yayi bayani tare da karin haske akan illar yawan amfani da wadannan magunguna ga lafiyar jikin dan Adama


Dr. Ladan yace “Illar maganinnan, kasan akwai wasu mutane masu ciwon zuciya, ko masu ciwon hawan jini, akwai wasu irin magunguna da suke sha, to idan aka hada wadannan magungunnan da shi wannan dakan maza da mutane ke sha, yakan saka zuciyar mutum ta samu illa. Kuma akwai wasu idan basu yi sa’a, sai su shafi idanunsu. To duk wadannan idan suka hadu taru, akwai illa sosai”


“Magungunan, abunda suke shine bude hanyar jinni. Wani lokacin sai ya bude hanyar jinin yayi yawa, yadda ba’a iya rike shi. Idan abun ya samu, babu yadda za’ayi a gyara abun”, in ji Dr. Ladan.Dr. Ladan ya bada shawara. “Abunda zan cewa mutane shine, kafin ka soma amfani da maganin, ka je kayi magana da likitanka, ya duba ya tabbatar baka da wani larura kuma, musamman yawancin mu kasan muna da irin ciwon zuciya, da ciwon hawan jini, bamu san muna da su ba”.


Hukumar kula da magunguna da abinci ta Najeriya, wato NAFDAC ta koka akan yadda ‘yan Najeriya ke yawan amfani da magungunan jima’i na turawa.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies