Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Ronaldo Zai Bar Real Madrid A Karshen Wannan Kakar


Rahotanni sun bayyana cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Cristiano Ronaldo ya yanke shawarar barin kungiyar a karshen wannan kakar.

Ronaldo, wanda shine dan wasan dayafi kowanne dan wasa zura kwallo a raga a tarihin kungiyar ya sanar da shugaban gudanarwar kungiyar cewa zai bar Madrid din idan kaka ta kare.

A kakar wasan data gabata ne dai rahotanni suka bayyana cewa dan wasan ya nuna aniyarsa a fili ta barin kungiyar kafin daga baya ya canja shawara ya zauna a kungiyar.

Wasu daga cikin dalilan dan wansan na barin kungiyar sun hada da tuhumar da hukumomin kasar ta sipaniya ta taba yi masa akan rashin biyan haraji da kuma gazawar kungiyar na kasa siyan Kylian Mbappe daga Monaco wand daga baya Parsi Saint German ta karbi dan wasan a matsayin aro da sharadin za ta biya kudin dan wasan a kakar wasa mai zuwa.
Dan wasan dai tun bayan komawarsa kungiyar ya taimakawa kungiyar ta lashe kofuna 13 ciki har da kofin zakarun turai guda uku da kuma gasar laliga guda biyu sannan a yanzu haka ma zasu buga wasan karshe na cin kofin zakarun turai da kungiyar Liberpool a wannan watan.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies