Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Wata Mata Ta Yi Ajalin Maigidanta Ta Hanyar Fafe Masa Tumbi Da Yanke Masa MazakutaRundunar ‘yan sanda ta na bincikar lamarin wata mata mai shekaru 47, wacce ake zargi ta kashe mijinta, ta hanyar yanke masa ‘yayan hanji da mazakuta.
Matar mai suna Udeme Odibi dai yar jahar Lagos ce.

Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin ta aikata laifin ne akan maigidanta mai suna mista Otike Odibi mai shekaru 50 a gidan su da ke unguwar Diamond Estate a yankin Sango-Tedo.


Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sandan jahar ya fitar, ya ce an cafke matar lokacin da take yunkurin kashe kanta.
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce a ranar 3 ga watan Mayu, ‘yan sanda sun samu bayanan cewa an kashe Otike a gidansa, kuma ana zargin matarsa ce ta aikata haka.
“Bayan samun wannan bayani, an tura jami’an ‘yan sanda wajen, inda suka samu mutum kwance cikin jini shabe-shabe, cikinsa a farke kuma hanjinsa a waje.

“Hakan bai isa ba, matar sai ta yanke azzakarinsa, sannan ta ajiye a hannunsa na dama.”

Rahotanni sun bayyana cewa Otike ya auri Udeme ne shekaru 3 da suka gabata, kuma ta aikata wannan abu a kan shi ne saboda ta bukaci ya rubuta wasiyyar da zai sanya ta ta gaje shi ita kadai, lamarin da Otike ya ki yarda, saboda ya na da ‘ya guda daya daga auren shi na baya.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies