Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Abinda Yakamata Ku Sani Game Da Zuwan Ali Nuhu Kasar RussiaSarkin Kannywood ya hadu da shahararen mai tsaran ragar kungiyar Real Madrid, Kaylor Navas, tare da da wasan kungiyar Arsenal, Joel Campbell.

Yan wasan Costa rica da jarumin ya hadu dasu basu yi nasara kubutar da kasar su wanda abokan adawar su suka yi nasara.
Tauraron fim ya hadu da sune bayan wasan su da kasar Sweden wanda aka tashi 1-0 a madadi Sweden.

Gabanin wannan saduwar, jarumin ya kalli wasan Nijeriya kai tsaye daga filin Kiliningard.

Kafin a fara wasan, ya hadu da yan wasan Super eagles, Abdullahi Shehu da Ahmed Musa inda ya saka hoton siu tare tare da yi masu fatan samun nasara

Sai dai Nijeriya bata yi nasara a wannan wasan ba domin, abokan wasan su Croatia ta lallasa su da kwallo biyu a raga.
Gasar na cigaba da gudana har yau kuma Nijeriya na shirin karawa da kasar Iceland ranar 22 ga wata wasan su na biyu a gasar.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies