Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Ba ni da ra'ayin shiga siyasa - Inji Ali Nuhu


Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Ali Nuhu, ya ce ba zai taba shiga harkokin siyasa ko tsayawa takara ba, duk kuwa da irin farin jini da daukakar da yake da ita.
A wata hira da ya yi da wakilin BBC na sashen Turancin Buroka, Mansur Abubakar, jarumin ya ce:
"Ba ni da ra'ayin siyasa ko kadan, ni fim ne sana'ata ba siyasa ba."
An kuma tambayi Ali Nuhu wanda suka yi hirar a yayin da suke daukar wani fim a Kano, ko zai iya shiga fina-finan kasar Amurka na Hollywood a nan gaba kamar yadda yake yin na Kudancin Najeriya?
din da ya biyo ta hanyata in dai an min tayinsa to zan shiga, in dai har ina jin harshen da za a yi fim din da shi," a cewar jarumin.
Ya kara da cewa; Ga masu cewa ba sa ganina a baya-bayan nan a fina-finan Kudancin Najeriya, to sai dai idan ba sa kallon sabbin fina-finai ne don ba a dade ba ma na yi wani fim mai suna "Banana Island."
Kula da iyali
An tambayi Ali Nuhu koyana samun isasshen lokacin da yake kula da iyalinsa ganin cewar sana'ar tasu mai cin lokaci ce?
Sai ya ce "Kwarai ina samun lokacin da nake zama da iyalina da kuma kula da su sosai, musamman a wannan lokaci na azumin watan Ramadan, tun da ba mu faye dadewa a wajen al'amuran daukar fim ba."
Ali Nuhu ya kuma shawarci matasan Najeriya da su yi koyi da abokinsa Ahmed Musa, dan wasan tawagar kwallon kafa ta Najeriya, kan yadda yake taimaka wa marasa galihu a lokacin Ramadan a jihar Kano.
bbchausa.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies