Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Buhari ba Allah ba ne, tsige shi za mu yi – Jagaba


Wani dan majalisar wakilan Najeriya ya bayyana cewa babu abun da ake fama da shi a mulkin Shugaba Muhammadu Buhari da ya wuce yunwa da bakar wahala.

Kalaman Jagaba Adams Jagaba, wanda ke wakilatar Kachia da Kagarko daga jihar Kaduna, na zuwa ne bayan da majalisun kasa suka ka yi barazanar daukar mataki kan shugaban idan bai aiwatar da kudurorin da suka zartar ba.

A ranar Talata ne majalisun dokokin kasar suka amince da wasu kudurori 12 da suka ce wajibi ne gwamnatin Muhamadu Buhari ta aiwatar da su ko kuma su dauki mataki.

Sai dai har yanzu babu wani martani da fadar shugaban kasar ta mayar.

Amma rahotanni sun ambato wani dan majalisa mai goyon bayan shugaban, Muhammed Gudaji Kazaure, na cewa an dora wa wasu takwarorinsa alhakin fara yunkurin tsige shugaban, amma ba za su "bari ya yi tasiri ba".


Mista Jagaba ya ce idan har Shugaba Buhari bai aiwatar da kudurorin da suka bukata ba to za su tsige shi a bisa tsarin kundin mulkin kasa.

Ya kara da cewa ba sa shakkar yiwuwar hakan don "Buharin ba Allah ba ne kuma bai yi kama da Annabi ba, duk inda ya yi kuskure za mu take shi" in ji dan majalisar.

Ku latsa hoton da ke kasa don sauraron hirar Adams Jagaba da Yusuf Tijjani na BBC:

Zaman da majalisun dokokin suka yi dai na zuwa ne a lokacin da rashin jituwa ke kara fitowa fili tsakanin gwamnatin Muhammadu Buhari da kuma shugabannin majalisar.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies