Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Buhari ya sauya ranar dimokradiyya a NajeriyaShugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai karrama marigayi Moshood Abiola da babbar lambar yabon kasar a ranar Talata - wato ranar tunawa da zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993.

Ana ganin marigayi Abiola ne ya lashe zaben wanda gwamnatin mulkin soja ta wancan lokacin ta soke shi, kuma akasarin 'yan kasar na ganin shi ne zabe mafi sahihanci a tarihin siyasar kasar.

Shugaba Buhari ya ce zai bai wa marigayin babbar lambar girmamawama ta GCFR a ranar bikin tuna wa da ranar a mako mai zuwa, kamar yadda wata sanarwa mai dauke da sahannun shugaban ta bayyana.

Hakazalika ya ce daga bana ranar 12 ga watan Yunin ce za ta zama ranar dimokradiyya a kasar kuma ranar hutu a fadin kasar, maimakon ranar 29 ga watan Mayu.

Sai dai bai yi karin haske ba game da ko hakan na nufin an sauya ranar mika mulki ga sabuwar gwamnati, wanda ake yi duk bayan shekara hudu a ranar 29 ga watan Mayun.

Har ila yau ya ce zai bai wa Ambasada Baba Gana Kingibe, wato mutumin da ya tsaya a matsayin mataimakin shugaban kasa tare da Abiola, lambar girmamawa ta GCON.

Hakazalika za a bai wa marigayi Gani Fawehinmi wato wani babban lauya wanda ya yi ta fadi tashi game da ranar tunawa da zaben 12 ga watan Yunin.

Marigayi Abiola ya rasu ne a ranar 7 ga watan Yulin shekarar 1998.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies