Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Ina da shekara 13 akayi mani auren fari – Maryam GidadoShahararriyar jarumar nan da tauraronta ke hasanakawa a masana’antar Kannywood, Maryam Gidado wacce akafi sani da Maryam Babban ta yi tsokaci akan wani babi day a shafi rayuwarta.

A cewar Maryam ita bazawara ce domin ta taba yin aure har sau karo biyu. Jarumar ta bayyana cewa anyi mata auren fari tana da shekaru 13 a duniya kasancewarta Bafulatanar asali.

Ta kuma ta haifi ‘Yarta ta farko tana da shekaru 14 bayan shekara daya da aurar da ita ga mijin nata na fari.

Ta kuma kara yin aure inda anan ne ta haifi ‘Danta na biyu,sannan kuma ta bayyana cewa alokacin da take da cikin ‘Dan nata na biyu ne sai mijin ya gudu ya bar ta.

Daga karshe Maryam ta jaddada cewa burin ta ya cika a yanzu musamman a harkar fim sai dai kawai addu'an Allah ya bata miji nagari ta raya Sunnah.
A baya Majiyarmu ka rahoto maku cewa jarumi Nuhu Abdullahi ya jaddada soyayyarsa ga Fati Washa harma yace shi a shirye yake ya aureta.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies