Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Yadda Shan Maganin Kara Karfin Garkuwa Jiki ‘Vitamins’ Ke Da Illa Ga Lafiya Rahoto ta bayyana cewa wasu likitocin asibitin ‘St. Michael’ da wasu malamai a jami’ar Toronto da ke kasar Canada sun bayyana cewa mafi yawan magungunan da ake amfani da su domin kara karfin garkuwan jiki wato ‘Vitamins’ basa yin abin da ake tunanin sunayi.
Likitocin sun gano haka ne bayan binciken da suka gudanar kan wasu magugunan kara karfin garkuwa kamar su ‘Vitamin A, B1, B2, B3, B6, B9, C, D da E sannan da ‘Carotene,Calcium, Iron,Zinc, Magnesium da Selenium’.
“Binciken da muka gudanar ya nuna mana cewa wadannan magunguna maimakon su kara wa mutum karfin garkuwar jiki sai dai cutar da lafiyarsa suke yi da idan ba a kula ba mutum kan iya rasa ransa ma.”
“Yawaita amfani da su kan kawo cututtukan shanyewar bangaren jiki, ciwon bugawar zuciya da sauran su.”
A karshe Likitocin sun bayyana cewa za a iya samun sinadarorin kara karfin garkuwan jiki idan ana cin kayan itatuwa, kayan lambu da abinci masu kyau.
Likitocin sun yi kira da a guje wa shan ire-iren wadannan magunguna cewa hakan ne kawai mafita.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies