Home

Music

Video

Kanny

Tags:

An Nada Rarara darekta waka na kamfen din Buhari 2019Fitaccen mawakin siyasa da ya shahara wajen yi wa shugaba Muhammadu Buhari waka ya zama sabon darektan waka na kamfen din Buhari.
Bayan shi a kwai fitaccen mai shirya wasan kwaikwayo na Nollywood, wato Desmond Elliot a kwamitin.
Kwamitin da tsohon gwamnan jihar Barno sanata Ali Modu Sheriff zai shugaban ta na tattare da jiga-jigan ‘yan jam’iyyar APC da take bugun kirji da su.
Kamar yadda PR Nigeria ya ruwaito wannan kwamiti da bam yake da kwamitin da ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya ke jagoranta.
A kwamitin akwai, Mamman Daura, Boss Mustapha, Bola Tinubu, Matthew Mbu, Ahmed Sani, George Akume, Abdullahi Adamu, da sanata Ita Giwa.
Sauran sun hada da Honarabul Gudaji Kazaure, Ireti Kingibe, Ismaila Funtua and Abu Ibrahim.
Shi kansa shugaba Buhari na cikin wannan sabuwar kwamiti.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies