Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Za a karo jiragen yaki don aiki a jihar Zamfara – Abubakar SaddiqueBabban hafsan sjin saman Najeriya Saddique Abubakar ya bayyana cewa rundunar za ta karo helikwaftoci da jiragen yaki domin kara kaimi a aiyukkan tsaro da rundunar ke yi jihar Zamfara.
Abubakar ya fadi haka ne a garin Gusau ranar Laraba.
Abubakar yace ya ziyarci jihar ne domin samun bayanai kan aiyukkan samar da tsaro da rundunar sojin saman ke yi a jihar.
Ya kara da cewa a dalilin rashin tashar jiragen sama a jihar jiragen saman rundunar za su dinga tasowa ne daga jihar Katsina zuwa Zamfara da kewaye domin gudanar da aiyukkan su.
Yayi kira ga mutanen jihar da su taimaka wa jami’an tsaron da duk bayanan da zai taimaka musu wajen kamo mutanen da suka hana mutane walwala a jihar.
” Samun nasarar gudanar da aiyukkan tsaron da muke yi a jihar Zamfara zai yi tasiri ne kawai idan har muka sami cikakken goyon baya daga ku mutanen jihar. Saboda haka muna rokon ku da ku taimaka mana domin a sami nasara kan hakan

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies