Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Zamu Nuna ma Gwamnatin APC mu haifaffu ne - Naziru Sarkin wakaMawaki Nazeer M Ahmad ya fadi haka ne a shafinsa na Instagram a wani gajeren video da ya wallafa.
Yace  " Sako ne nake mikawa ga wannan gomnati ta APC dukda dai bazan fadi abinda tai mana yanzu ba sai daga baya amma dai ina shaida mata muda take ganin bamu isa a gode mana ba toh fa muma da ranarmu. Kuma mu matasanan da muka bada gudunmawa ga kafuwarta musamman ire irena matasan arewa zamu nuna mata cewa mu haifaffu ne.
Nazeer M Ahmad  dai shaharen mawaki ne na Hausa wanda yana daya daga mawakan da sukayita tallar Buhari 2015 saidai bayan hawan shugaban ya karkata akalarsa zuwaga DAUDA KAHUTU RARARA wanda kamar wani abokin karawa ne ga Sarkin waka. Ko acikin makonnan APC ta nada RARARA matsayin daraktan yada wakokin tallar buhari a zaben shekarar 2019.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies