Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Dalilan da suka sa mataimakin gwamnan Kano yin murabus


Gwmnatin jihar Kano ta ce mataimakin gwamnan jihar ya yi gaggawar yin murabus ne yayin da 'yan majalisa ke shirin tsige shi.
Mataimakin gwamnan na jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar wanda ya gabatar da takardar murabus din sa, ya zargi gwamnatin Ganduje da mayar da shi saniyar ware, tare da cewa wani lokaci da kudin aljihunsa yake amfani wajen gudanar da ayyukan gwamnati.

A baya-bayan nan ne tsohon mataimakin gwamnan ya shaidawa BBC cewa tsawon fiye da shekara biyu, zaman doya da manja yake tsakaninsa da Ganduje saboda yana ra'ayin Kwankwasiya. Ya kuma ce har ta kai ana yi rayuwarsa barazana.
A martanin da ta mayar, gwamnatin Ganduje ta musanta dukkanin zarge-zargen inda ta ce babu wani sabani ko bi-ta-kulli da ake yi wa tsohon mataimakin gwamnan.

Wata sanarwar da kwamishin watsa labarai na jihar Kano ya fitar ta ce gwamnatin ya yi murabus ne a yayin da 'yan majalisar jihar ke shirin tsige shi.

Sanarwar ta kuma musanta zargin da mataimakin gwamnan ya yi cewar ana tauye shi wajen fitar da kudaden alawus na tafiye-tafiye tare da yin barazana ga rayuwarsa.

Gwamnatin Kano ta ce " a 2017 kadai, Naira miliyan 120 aka kashe wa ofishin mataimakin gwamnan na alawus din tafiye- tafiyensa. A 2018 kuma an kashe ma sa Naira miliyan 30."
A cikin wasikar murabus din mataimakin gwamnan, ya ce ya so ya ci gaba da rike mukaminsa har zuwa karshen wa'adin mulkin da aka zabe su, amma ya sauka ne saboda matsalolin da suka dabaibaye dangantakarsa da gwamnan jihar:

"Ina sanar da kai cewa na yanke shawarar sauka daga mukamin mataimakin gwamnan jihar Kano daga ranar Asabar 4 ga watan Agusta, 2018.

A cikin wasikar, ya kara da cewa, "Idan ba ka manta ba mai girma gwamna, na sha jan hankalinka ga wasu batutuwa da ka iya tada husumar da muke fuskanta a yau, amma kokarin nawa bai yi nasara ba."

Gwamnatin Ganduje ta ce tana iya daukar matakin shari'a kan da zargin da tsohon mataimakin gwamnan ya yi cewar gwamnati za ta dauki nauyin shirya zanga-zanga domin nuna goyon baya ga bukatar tsige shi.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies