Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Kotu Ta Tasa Keyar Mutumin Da Ya Kashe Matarsa Da Duka Akan Naira 200 Zuwa Gidan KasoWani Henry Anaele da ya daki matarsa har sai da ta ce ga garinku nan ya gurfana a gaban kotun majistare da ke zamanta a Ebuta Meta a jiya Laraba.
Henry mai shekaru 40 da haihuwa ya hau matarsa da duka ne akan wai wani mutum ya bata kyautar Naira 200 kuma ta karba ta yi godiya.
Babban mai shari’a na kotun, O.O. Olatunji ya bayar da umarni da a garkame Henry a gidan yari na Ikoyi kafin kotu ta samu shawarar yadda za ta yi da shi daga daraktan sauraren kararraki da koken jama’a na jihar.
Mai shigar da kara a madadin gwamnati, Insfecta Cousin Adams ya bayyanawa kotu cewa Henry ya aikata laifin da a ke zarginsa da shi ne a ranar 15 ga watan Yuni da misalin karfe 11:45 na dare a gida mai lamba 72, a rukunin gidaje na Goodness da a ke a Satellite Town, jihar Legas.
Cousin Adams ya shaidawa kotu cewa, Henry ya hau matarsa da jibga ne bayan da ya fahimci cewa wani mutum ya yi wa matarsa Chinyere mai shekaru 35 kyautar Naira 200.
Laifin na Henry ya saba kundin manyan laifuka sashe na 223 na jihar Legas shekarar 2015, inda laifin ke da hukuncin kisa ga wanda ya aikata shi
Mai shari’a O.O. ya daga sauraren karar zuwa ranar 6 ga watan Ogusta, 2018.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies