Test Footer

Boko Haram: Dogarin Shekau da ya tuba yayi fallasa da tonon silili


Boko Haram: Dogarin Shekau da ya tuba yayi fallasa da tonon silili Daya daga cikin matasan da suka ce an yaudare su wajen shigar da su kungiyar nan ta ta'addanci da ake wa lakabi da Boko Haram da kuma yanzu ya tuba yayi fallasa da tonon silili a cikin wata fira da yayi da wakilin majiyar mu. Shi dai wannan matashi wanda ya bayyana cewa shi ne dogarin daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar ya ce shi sunan sa Bara Umara kuma shekarun sa 27 a duniya sannan kuma ya kara da cewa ya fito ne daga cikin dajin Sambisa. NAIJ ta samu cewa tubabben dan ta'addar ya kuma ci gaba da cewa shi dan asalin garin Banki ne inda kuma ya bayyana yadda ya shiga cikin kungiyar ta Bako Haram ta hannun wani abokin sa. Matashin ya kuma bayyana cewa ya yi ta zuwa yake-yake har sau shida a gaba da Bama da a garuruwan Wulari da Bita da gefen Tafkin Chadi haka ma kuma yace idan sojoji su ka shiga dajin Sambisa su ne kan kai masu hari.

0 Response to "Boko Haram: Dogarin Shekau da ya tuba yayi fallasa da tonon silili "

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel