Test Footer

Maniyyata 2 na jihar Sokoto sun yi tsintuwar makudan kudi a kasa mai tsarki


Maniyyata 2 na jihar Sokoto sun yi tsintuwar makudan kudi a kasa mai tsarki Na gari dai ba su karewa domin kuwa wasu maniyyatan jihar Sokoto sun yi tsintuwar makudan kudi a kasa mai tsarki kuma sun maishewa mai wannan kudade abin sa. Wasu maniyyata biyu na jihar Sokoto sun yi tsintuwar kudi na Dalar Amurka 700, Sefa ta Nijar 15,000 da kuma riyal na Saudiya 137 a kasa mai tsarki, kuma sun mayarwa da mai shi wanda shima maniyyacin jihar ne. Daya daga cikin maniyyatan, Dauda Ibrahim, daga karamar hukumar Gwadabawa dake jihar ta Sokoto, ya bayyana cewa, sun yi tsinyuwar wannan kudin ne a hawa na biyu na Otel din Rhoda, inda daman nan masauki da aka tanadarwa maniyyatan jihar Sokoto wanda yake unguwar Masfalah a can kasa mai tsarki.

Mallam Dauda, wanda manomin albasa ne, ya bayyanawa manema labarai na DAILY TRUST cewa, da kyar ya samu ya cika kudin kujerar sa ta tafiya aikin Hajjin bana, amma tsintuwar wannan kudi bat sanya shi ya so zuciyar sa ba.

Wani shehun malami, Sheikh Umar Maidamma Shagari, ya yabawa wadannan maniyyatan biyu kuma ya tabbatar mu su da cewa akwai sakayya mai tsoka daga wajen Mahaliccinsu. Ya kara da cewa, hukumar jin dadin Alhazai, ta binciko mai wannan kudade, Shu'aibu Usman, na karamar hukumar Isa dake jihar ta Sokoton dai, kuma ta mayar ma sa da kudaden sa. A yayin haka dai, an hadawa wata mata gudunmawar riyal 500 da ta batar da guzurinta a can kasa mai tsarki.

0 Response to "Maniyyata 2 na jihar Sokoto sun yi tsintuwar makudan kudi a kasa mai tsarki "

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel