Test Footer

Wani malamin islamiya a kotu bisa zargin lalata da daliban sa 3


Wani malamin islamiya a kotu bisa zargin lalata da daliban sa 3 Wani al'amari mai kama da almara da kuma tashin hankali ya afku a karamar hukumar Ikeja ta jihar Legas inda iyayen wasu yan mata uku da shekarun su bai haura sha biyu ba suka maka malamin islamiyar su a kotu bisa zargin yin lalata da. Mahaifin yaran mai suna Clifford Ogu wanda ya shigar da karar a gaban kotun ya shaidawa alkalin cewa malamin ya aikata wannan ta'asar ne tun daga watan Mayu har zuwa watan Agustan wannan shekarar inda kuma yace malamin na samun damar hakan ne a duk lokacin da yazo yi masu karatun harshen Larabci a gidan su.

NAIJ.com ta samu cewa shi kuma a nasa bangaren tuni malamin na Islamiya ya karyata wannan zargin da ake yi masa inda kuma ya ne tsarin Allah daga aikata dukkan alfasha. Alkalin kotun Taiwo Akanni ya bada belin malamin kan Naira 250,000 tare da shaidu biyu wanda malamin zai kawo sannan ya daga shari’ar zuwa 11 ga watan Satumba.

0 Response to "Wani malamin islamiya a kotu bisa zargin lalata da daliban sa 3 "

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel