Test Footer

Wata 'yar shekara 16 ta bayyana yadda maza 7 suka fyade ta


Wata 'yar shekara 16 ta bayyana yadda maza 7 suka fyade ta LATEST SPORTS GOSSIP WEDDINGS CELEBS HAUSA NEWS ANNOUNCEMENTS FEEDBACK 367 USD/NGN Kashedi! Yanzu haka Sojin Najeriya na bibiyar abunda kuke yadawa a dandalin sada zumunta Advertise with us Wata 'yar shekara 16 ta bayyana yadda maza 7 suka fyade ta Author: Ishaq Ismail UPDATED: AN HOUR AGO VIEWS: 1825 Category: News SHARE ON FACEBOOK SEND VIA EMAIL SEND ON WHATSAPP SHARE ON FACEBOOK SEND VIA EMAIL SEND ON WHATSAPP A can jihar Delta kuma, wata budurwa ta bayyana sunayenn maza bakwai da suka yi ma ta ta karfin tsiya suka keta mata haddi Hukumar 'yan sanda ta cafke wasu mutane da laifin yiwa 'yar shekara 16 fayde a makarantar Firamare ta Okene a yankin Okuokoko dake karamar hukumar Okpe a jihar Delta. Wasu mutum biyar da aka aikata wannan laifin da su sun yi na zomo kuma jami'an yan sanda sun bazama wajen neman su.. Shafin DAILY POST ya ruwaito cewa, wadanda suka aikata wannan ta'asa sun dauki bidiyo da hotunan a yayin da suke aikatawa wannan budurwa masha'a da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar 8 ga watan Agusta.

Wadda wannan ibtila'i ya sauka a kanta, ta bayyanawa manema labarai a garin Warri dake jihar ta Delta cewa, tana tuna lokacin da mutum bakwai su ka yi ma ta ta karfe suka ja ta cikin wata makaranta a yayin da take kan hanyar ta ta zuwa ziyartar abokiyarta. Ta ce gangamin mutanen sai da suka kece kayan jikinta gaba daya sannan suka yi lalata da ita daya bayan daya.

Shugaban kungiyar na kare hakkin dan Adam na jihar Delta, Kwamared Prince Kehinde-Taiga, ya yi tir da wannan abu kuma ya bayyana cewa kungiyar ba za ta zauna ba har sai ta ga an hukunta wannan mutane 7 domin nemawa budurwar hakki da adalci.

0 Response to "Wata 'yar shekara 16 ta bayyana yadda maza 7 suka fyade ta "

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel