Test Footer

Badaƙalar Dawo Da Maina: Asiri Ya TonuA daidai lokacin da abubuwa ke sake fitowa dangane da badaƙalar dawo da tsohon jagoran ‘yan fansho bakin aiki, Mista Abdulrasheed Maina aiki, a jiya ne asiri ya tonu inda aka sami Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami (SAN) da murguɗa hukuncin Babbar Kotun Tarayya, ta yadda lamarin ya yi daidai da iya dawo da Maina aikin gwamnati.
Babban Lauyan Gwamnatin a wata wasiƙa wacce aka rubuta ta a ranar 27 ga watan Afrilun 2017, wacce kuma a cikinta ya umurci ofishin Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da ta mayar da Maina a bakin aiki, bisa dogaro da hukuncin da Mai Shari’a Adamu Bello na Babbar Kotun Tarayya yayi.
Kotun wacce ta zauna a ranar 27 ga watan Maris ɗin 2013 a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Sau biyu Malami yana bayar da umurnin a mayar da Maina a bakin aiki a matsayin Darakta a Hukumar Ma’aikata ta Tarayya, bisa dogaro da cewa Mai Shari’a Bello ya yi wanke Mainan daga farautarsa da jami’an ‘yan sanda suke yi.
Sai dai an yi zargin cewa, a wasiƙar tasa, Ministan Shari’a Malami ya kawar da kai daga zargin sama da faɗin Naira Biliyan biyu da ake yi wa Maina, wanda a kansu ne hukumar EFCC ta ke tsaka da bincikensa. Haka nan kuma an zargi wasiƙar Malami da ƙin yin ƙarin bayani dangane da wannan farauta ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa. Haka kuma wasiƙar ta ƙi yin bayanin irin yadda Mai Shari’a Bello ya shawarci Maina da ya miƙa kansa ga hukuma don a ci gaba da bincike, wanda hakan zai wanke shi daga buhunan zargin da ke kansa. Wasiƙar wacce take da lamba kamar haka; ‘HAGF/FCSC/2017/Ɓol. 1/3’, kuma wacce Malamin ya rubuta wa Hukumar Ma’aikata ta Tarayya, ta na ɗauke da take kamar haka, ‘Bin diddigin batun mayar da Mista Abdurrasheed Maina a bakin aiki, a matsayin darakta a Hukumar Ma’aikata ta Tarayya.
“Wasiƙarku mai lamba ‘FCSC/CHMN/OC/17/Ɓol. ƊIƁ/209’ wacce kuma aka rubuto ta a ranar 3 ga watan Maris 2017, kuma wasiƙun waɗanda aka aike da samfurinsu zuwa ga ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya dangane da lamarin, daga ofishin Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, wasiƙar mai lamba HCSF/LU/COR/FCSC/749/III/84 wacce aka rubuta ta a ranar 27 ga watan Maris 2017. “Idan ba ku manta ba, na rubuto wa ofishinku wasiƙa mai lamba HAGF/FCSC/2017/Ɓol. 1/2 a ranar 21 ga watan Fabrairun 2017, wacce a cikinta na janyo hankalinku dangane da hukuncin Mai Shari’a A. Bello na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja wanda ya yanke a ranar Laraba 27 ga watan Maris 2013 a shari’a mai lamba FHC/Abj/CS/65/13 (tsakanin Abdulrasheed Maina da Majalisar Dattawan Nijeriya da wasu hukumomi takwas), shari’a wacce ofishina ya wakilci gwamnatin tarayya. “A wasiƙa ta, na umurce ku da ku yi aiki da hukuncin kotun da ya kore farautar da hukumar ‘yan sanda ke yiwa Dakta Abdulrasheed A. Maina, wanda kuma wannan farauta ne ya haifar da tuhumarsa mai lamba MI/30040/1/1, wanda aka rubuta a ranar 15 ga watan Fabrairun 2013, wanda ya zama sanadin sallamarsa daga aikin gwamnati a ranar 5 ga watan Maris 2013. ” Inji wasiƙar Malami.
Source :-Leadershipng

0 Response to "Badaƙalar Dawo Da Maina: Asiri Ya Tonu"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel