Test Footer

Buhari ya yi taka-tsan-tsan wajen fitar da sunayen Barayin gwamnatiWani dan majalisar dattijai ya yiwa gwamnatin tarayya kashedin sanya sunayen mambobin jam'iyyar APC da makarraban shugaba Buhari cikin sunayen barayin gwamnati da za ta fitar na kwana-kwanan nan.
Shehu Sani wanda shine dan Majalisar na jam'iyyar APC mai wakiltar Tsakiyar jihar Kaduna ya bayyana cewa, sunayen barayin gwamnati da ake hadawa domin wallafa su a jaridu su kasance sun kunshi mambobin jam'iyyar APC ba na jam'iyyar PDP kadai ba.
Dan Majalisar na Dattijai ya bayyana hakan ne a ranar Jumma'ar da ta gabata a shafin sa dandalin sada zumunta na facebook.
Shehu ya bayyana cewa, "Yanke hukuncin gwamnatin tarayya na wallafa sunayen barayin gwamnati abu ne da ya cancanci yabo. Ina kyautata zaton jerin sunayen ba zai takaita akan sunayen 'yan wasa na kungiyar lema ba, face zai kun shi har da 'yan wasa na kungiyar tsintsiya da 'yan wasa na makarraban gwamnatin tarayya.
" Dattijon ya yi amfani da tsintsiya a matsayin jam'iyyar APc da kuma jam'iyyar PDP a matsayin lema.
Idan ba a manta ba, shugaba Buhari ya bayar da umarni ga cibiyoyi da ma'aikatun gwamnati akan su tattaro sunayen barayin gwamnatin domin wallafa su a jaridu.

0 Response to "Buhari ya yi taka-tsan-tsan wajen fitar da sunayen Barayin gwamnati "

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel