Test Footer

Dandalin Kannywood: Barayi sun haura gidan jarumi Suleiman BoshoLabaran da muke samu daga masana'antar Kannywood na nuni da cewa wasu bata garin mutane sun haura a gidan fitaccen jarumin fina-finan Hausa musamman ma a fagen barkwanci watau Suleiman Bosho. Haka ma dai kamar yadda muka samu daga majiyar ta mu wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar Asabar din da ta gabata amma sai dai mun samu tabbacin cewa barayin ba su samu nasarar daukar wani muhimmin abu ba mai anfani sosai daga gidan.
Majiyarmu ta samu dai cewa barayin da zuwa yanzu bamu san adadin yawan su ba sun haura ne cikin gidan da dare kuma suka shiga wani daki suka hargitsa shi da nufin su samu abun da suke so amma sai ba su samu ba.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ma dai mun kawo maku labarin cewa jarumin ya koka da yadda a kullu yaumin yake ta kara samun masu yi masa bakin ciki da hassada da ma a wasu lokuttan kage.

0 Response to "Dandalin Kannywood: Barayi sun haura gidan jarumi Suleiman Bosho "

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel