Test Footer

Honarable Gudaji Kazaure ya caccaki shugaba Buhari a kaikaiceFitaccen dan majalisar wakillan nan na Najeriya mai wakiltar mazabar Kazaure, Roni, 'Yankwashi da kuma Gwiwa dukkan su a jihar Jigawa dake a Arewa maso yammacin Najeriya mai suna Honarable Muhammad Gudaji Kazaure ya caccaki shugaba Buhari a kaikaice.
Shahararren dan majalisar dai ya yi wannan caccakar ne a yayin da yake tsokaci a zauren na majalisar game da sabon tsarin nan na gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Buhari din da ke fitar da doyar da aka noma zuwa kasashen ketare.
Hausazone.com dai ta samu cewa ta yake tsokacin, Alhaji Gudaji Kazaure ya nuna rashin dubara da kuma sanin ya kamata daga bangaren gwamnatin game da wannan tsarin inda yace shi baiga yadda za'ayi talaka ya mori wannan irin bahagon tsarin ba na fitar da kayan abinci zuwa kasashen waje sannan kuma an hana shigowa da shi.
Dan majalisar daga karshe sai ya jawo hankanin shugabannin majalisar yan uwansa da ma sauran shugabannin kasar a dukkan matakan mulki da su duba wannan matsala domin kawo gyara.

0 Response to "Honarable Gudaji Kazaure ya caccaki shugaba Buhari a kaikaice"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel