Test Footer

Jihohi 4 ne kawai ke iya biyan albashi ba tare da sun ciyo bashi ba a NajeriyaWata kungiya Inganta zamantakewan al'umma ta fitar da wani rahoto akan yanayin kudaden shiga da jihohin Najeriya ke tara wa - Sakamakon binciken ya nuna cewa jihohi 4 ne kawai ke da ingantatun hanyoyin samun kudin shiga da zasu iya biyan bukatun su - Har ila yau, rahoton ya bayyana jihar da tafi kowace bashi a halin yanzu Sakamakon wani bincike da wata kungiya mai rajin inganta zamantakewan al'umma mai suna BudgIT ta gudanar a shekarar 2017 ya nuna cewa jihohi 4 ne kawai a Najeriya ke iya biyan albashin ma'aikatan su ba tare da sun ciyo bashi ba. Jihohin da binciken ya nuna suna iya biyan bukatun nasu dai sune jihohin Kano, Katsina, Rivers da kuma jihar Legas da ke kan gaba. An kammala tatara sakamakon binciken ranar Alhamis amma sai rannan Juma'a aka fitar dashi bainar jama'a.

KARANTA:- Yadda mukeyi da kudinda muka karbo daga Barayin gwamnati-Gwamnatin nigeria

Abin da binciken yayi la'akari dashi shine jimlan kudaden shiga da jihohin suke samu a kowane wata da kuma kudaden da suke kashewa a kowane wata.

KARANTA:- Yadda momo ya kunyata umma shehu a wata hira da sukayi

Har ila yau, binciken ya duba yanayin yadda jihohin ke karban haraji domin biyan basusukan da ake binsu. Jihar Osun itace tafi kowane jiha bashi a Najeriya domin binciken ya nuna cewa babu ingantatun hanyoyin tattara haraji a jihar. Jihohin Kwara, Delta, Kebbi, Gombe da Ebonyi kuma suna kara inganta hanyoyin tattara harajin nasu wadda hakan na nufin a nan gaba zasu iya zama cikin jihohin da ka iya biyan bukatun su ba tare da ciyo bashin ba.

0 Response to "Jihohi 4 ne kawai ke iya biyan albashi ba tare da sun ciyo bashi ba a Najeriya "

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel