Test Footer

Rahama Sadau ta nemi afuwan ƙungiyar yan Fim ta ƙasaFitacciyar jarumar fina finan Kannywood din nan data shahara wajen iya tikan rawa kamar mazari, Rahama Sadau ta nemi afuwar kungiyar kula yan Fim ta kasa, MOPPAN dangane da dakatar da ita da suka yi. Premium Times ta ruwaito tun a shekarar data gabata ne MOPPAN ta sallami Rahama Sadau daga harkar Fim sakamakon wani bidiyon waka data fito a ciki, wanda aka hangeta tana rungumar wani mawaki mai suna ClassiQ. Majiyar NAIJ.com ta ruwaito wasikar da Rahama Sadau ta aike ma MOPPAN na neman afuwa na kunshe da magiya tare da nuna nadamar abubuwan da suka faru a baya, inda ta roki a mayar da ita harkar Fim. Sai dai sallamar da aka yi ma Rahama Sadau ya kara haskaka tauraron ta, inda shahararren mawakin kasar Amurka, Akon ya gayyace ta zuwa Amurka don samun gurbi cikin wani Fim dinsa. “Dan Adam ajizi ne, don haka zan iya yin kuskure, don haka a matsayita na yarinya, ina rokon kafatanin yan Fim, shuwagabannin kungiyoyin Fim, al’ummar Arewa da kuma yan kallo daku yafe min,” Inji Rahama. Sakataren MOPPAN, Salisu Mohammed ya bayyana ma majiyar mu cewa “Zamu yi zaman tattauna wasikar tat a, don daukan matsaya guda akan batun. Amma fa tayi maganganu marasa dadi a baya, wanda basu dace ba.”

0 Response to "Rahama Sadau ta nemi afuwan ƙungiyar yan Fim ta ƙasa"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel