Test Footer

Saboda Adam A Zango Na Shigo Nigeriya Kuma na Fara Fim Inji Amina MuhammadSunana Amina Muhammadu, daga ƙasar Kamaru na zo Nijeriya. Na yi karatuna tun daga furamare har sakandire a Kamaru, duk cikin harshen Faransanci. Daga bisani na halarci wata tsangaya da ake koyar da Turanci a can Kamarun, na koya cikin wata uku. Yanzu ina jin yare huɗu, Fulfulde, Hausa, Faransanci da kuma Turanci. Wannan shi dai a taƙaice. Ta yaya aka yi kika zo Nijeriya?
To, lokacin da nake Kamaru ina kallon finafinan Hausa, kuma ina jin daɗin yadda ake nuna al’adar Hausa. Na koyi abubuwa da yawa dalilin fim ɗin Hausa, tun daga kan sanya sutura irin su; atamfa, abaya, leshi da sauran su. Haka zalika, salon maganganun da ake amfani da su, suna matuƙar birge ni. Don nakan kwaikwayi abubuwa da dama. Jarumin da nake matuƙar ƙauna shi ne Adam A Zango, saboda shi na baro Kamaru na zo Nijeriya. Na daɗe ina mafarkin yin ido biyu da shi, nagode Allah da ban mutu ba sai da Ya cika min burina na ganin Zango, har na yi fim da shi.
Da ma saboda fim kika zo?
Eh to, kai tsaya ba zan ce saboda fim na zo ba, na zo ne saboda in ga Adam A. Zango, sai bayan mun haɗu na ji ina sha’awar fitowa a fim. Kuma, dalilin fitowa ta fim ɗin shi ne, ƙalubalen da na gamu da shi kafin iyayena su yarda su bar ni yana da yawa. Amma dai sun ƙyale ni, tun da sun fahimci abin da nake so kenan. Saboda haka, ta ya ya zan gamsar da su cewa na haɗu da shi, shi ne in yi fim ɗin da zan kai musu su gani. Hatta ƙawayena ta hanyar fim zasu yarda na gan shi. Tsoron da iyayena suka riƙa ji bai wuce yadda ba ni da kowa a Nijeriya ba, ba su san hannun wanda zan faɗa ba. Sai na nuna musu cewar Adam A. Zango yana da kirki kuma zai kula ni, duk ban taɓa haɗuwa da shi ba, na yi iya bakin ƙoƙarina wajen gamsar da su; duk da ina matsayin mace, zan kiyaye mutuncina har in dawo gida. Na faɗa musu duk da ban ga shi ba, ballantana in san halayensa na zahiri, amma na san Inn Shaa Allah zai karɓe ni hannu biyu-biyu.
Wane ƙalubale kika haɗu da shi a hanya? Taɓ! Gaskiya na sha wahala ba ƙarama ba, domin mota na biyo ba a jirgi na zo ba. Na shigo Nijeriya ne ta jihar Ribas, na kwana a Kalaba, saboda matsalar tsaro da ake fama da ita a Arewa Maso Gabashin Nijeriya. Da gari ya waye na samu motar Abuja, sannan na shigo Kaduna.
Lokacin da na zo Arewa ban san kowa ba, ga shi ba na jin Hausa, ba kuma kowa ne yake cin Turanci ba. Da ma iyayena sun bani kuɗi isassu kafin na taho, saboda haka na kama otel a Kaduna na zauna, na fara tunanin ta inda zan fara.
Lokacin da yunwa ta kama ni, na sa aka kawo min abinci, sai da na yi kuka har kaina ya yi ciwo, don ban taɓa cin irin abincin ba; shinkafa da wake ce.
Amma yanzu na saba.
Yadda kuwa aka yi na san Adam yana Kaduna shi ne, kullum a waƙoƙinsa yana yawan faɗar garin Kaduna a matsayin inda yake tinƙaho da shi, shi yasa kai tsaye na nufin can. A hankali na haɗu da wani Guyson, wanda yaronsa ne, sai ya ga hotonsa a wayata, sai ya ce na san shi ne, sai na ba shi labarin yadda aka yi na zo Nijeriya.
Daga bisani sai na haɗu da Habu Sarki, wanda kusan amini ne a wajen Zango, shi ya kula ni, ya ɗauke ni tamkar ƙanwarsa ta jini, har Allah ya sa na haɗu da Adam A. Zango. Haƙiƙa ba zan manta da gudunmuwar Habu Sarki gare ni ba, ya taimake ni sosai, shi ne kallo a matsayin ubangidana.
Ta yaya kika fara fim, kuma kin yin fim ya kai nawa? Lokacin da zan fara fim na gami da matsaloli da yawa, na farko ba na jin Hausa, kuma fim ɗin nan da Hausa ake yi. Saboda haka sai da na shafe wata shida ina koyon harshen Hausa.
Haƙiƙa na yi farin ciki ƙwarai kuma ina alfahari da finafinai Kannywood, ga shi dalilinsa na koyi harshe da al’adun wani gari da ba nawa ba.
Da aka zo za a fara fim ɗin, sai aka ji hausata ba ta gama zama gangariya ba, sai aka ƙara min wasu watannin.
Cikin ikon Allah na koyi harshen Hausa, na yi fim ɗin na farko mai suna AMAL. Bayan shi na yi finafinai guda biyu, Hisabi da Matan Aure.
Har ila yau, lokacin da za a yi min fim ɗin da yawa suna cewa rol ɗin bai dace da ni ba, to kuma sadda aka ɗora min kyamara sai tsoro ya mamaye ni, sai da aka yi da gaske, domin ana so in yi, tukun na zage aka yi aikin da ni. Dama kuma an faɗa min, kusan duk waɗanda suka Kannywood da farko sai sun fuskanci wannan matsalar, amma a hankali sai ta zama tarihi.

0 Response to "Saboda Adam A Zango Na Shigo Nigeriya Kuma na Fara Fim Inji Amina Muhammad"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel