Test Footer

Sani musa Danja shahararren Jarumin Kannywood ya zama jakadan majalisar dinkin duniyaAnyi taro kaddamar dashi da sauran shahararren yan wasan fannin nishdantarwa a garin Abuja Fittaccen dan wassan kwaikwayo kuma mawaki Sani Danja ya samun sabon mukami a majalisar dinkin duniya inda aka nada shi a matsayin jakada a fannin kafa manufa ta samun cigaban zamani (SDGs) ta majalisar. Anyi taron kaddamar da jarumai a garin Abuja ranar laraba 25 ga watan octoba yayin da ake bikin nuna farin ciki zagoyowar ranar majalisar dinkin duniya. Danja wanda aka fi sani da 'sarkin nishadi na arewa' ya shahara a fadin Nijeriya bisa ga rawan da yake taka wa a harkar nishadantarwa. Wannan sabon daukaka yana cikin jerin jakadanci da ya samu daga kamfanin Glo, Rotary, gidauniyar save the children, western loto da sauran su. Banda Sani Danja sauran jaruman kannywood da suka samu mukamin jakadanci na majalisar dinkin duniya akwai Yakubu Muhammed da Uzee Usman. A cikin manyan baki da suka halarci taron akwai Ministan wassannin da ayyukan matasa Solomon Dalung da babban mataimakin shugaban kasa a kan SDGs Princess Adejoke Orelope-Adefulire. Sauran jaruman Nijeriya da suka samu matsayin sun hada da mawaki Tuface, Sunny Ade, Omotola jalade Ekehinde, Chigurl, Teju babyface, Alibaba da Zdon Paporella.

0 Response to "Sani musa Danja shahararren Jarumin Kannywood ya zama jakadan majalisar dinkin duniya"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel