Test Footer

Wata Jarumar kannywood ta samu sarauta


Fitacciyar jarumar masana’anta dake shirya fina-finan hausa ta Kannywood Rashida Adamu Abdullahi wanda aka fi sani da Rashida Mai sa’a ta samu sarauta. Kungiyar masu shirya fina-finai ta arewa na Arewa film makers association ta nada ta a matsayin ‘Wakiliyar Arewa’.

Wakiliyar Arewa Tare Da Gimbiyar Arewa Bikin nadin sarautar wanda aka gudanar a jihar Niger ya samu halartar manyan baki da dama ciki har da jaruma Hadizan Saima. Ita ma mawakiya Binta Labaran wanda aka fi sani da Fati nijar ta samu sarautar ‘Gimbiyar Arewa’ a bikin nadin wanda aka gudanar a garin Minna babban birnin jihar Niger.
Fati Nijar CE Gimbiyar Arewa Su jaruman sun nuna farin cikin su bisa ga wannan mukami da suka sami a shafukan su ta kafafen sada zumunta inda suma masoyan su suka tofa masu albarka tare da yi masu fatan alheri tare da jinjina masu.
Pulse.ng/hausa

0 Response to "Wata Jarumar kannywood ta samu sarauta"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel