Test Footer

Yadda ake amfani da kungiyoyi wajen satar kudaden - Ngozi Okonjo-IwealaNgozi Okonjo-Iweala ta yi bankada cewa mafi yawan barayin gwamnati suna amfani da kungiyoyi masu zaman kansu ne wajen satar kudade - Ta ce barayin gwamnati na bullo da sabbin dabaru wajen boye haramtattun kudade Tsohuwar Ministar Kudi ta Najeriya, Dakta Ngozi Okonjo-Iweala ta yi bankada cewa mafi yawan barayin gwamnati suna amfani da kungiyoyi masu zaman kansu ne wajen satar kudaden gwamnati. A cewar ta barayin gwamnati na bullo da sabbin dabaru wajen boye haramtattun kudade.
A baya Majiyarmu ta rahoto cewa tsohuwar Ministar ilimi ta kasar tace Shugaban kasa Buhari na kokarin rufe maganar badakalar da ta kunno kai a kamfanin NNPC amma kuma irin wannan batu ya fi karfin a gani ayi shiru har ta ke cewa kuma zargin ya shafawa Gwamnatin Shugaba Buhari da ke kokarin yaki da sata wani danyen tabo.
Oby Ezekwensili tayi kira da Shugaban kasar yayi wuf ya fara shirin binciken badakalar da ake zargi a karkashin NNPC. Madam Eze take cewa ba maganar ace an yi sulhu bane tsakanin Maikanti Baru da Ibe Kachikwu kamar yadda ta ga hotuna na yawo kwanan nan a shafin Tuwita.

0 Response to "Yadda ake amfani da kungiyoyi wajen satar kudaden - Ngozi Okonjo-Iweala "

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel