Test Footer

Yadda Yan Sanda Sun Cafke Dan Shekara 50 Da Ya Yi Wa 'Yar Shekara Uku Fyade Ta Rasu'Yan Sanda Sun Cafke Dan Shekara 50 Da Ya Yi Wa 'Yar Shekara Uku Fyade Ta Rasu A Katsina Daga Jamilu Dabawa Rundunar 'Yan sanda ta jihar Katsina ta yi nasarar cafke Abdullahi Sani, wanda aka fi sani da (Mai Aya) dan shekara hamsin a duniya dake unguwar Jabiri a karamar Hukumar Funtua da ya yi wa wata 'yar shekara uku mai suna Umma Ibrahim da suke unguwa daya a Jabiri fyade. A wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar DSP Gambo Isah ya rabawa manema labarai, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya aikata wannan mummunan aiki ne a cikin wani kangon gida, inda ya yi amfani da ita da karfi. DSP Gambo ya kara da cewa, bayan afkuwar lamarin an hanzarta kai Umma babban asibitin garin Funtua, amma daga bisani ta rasu a ranar Juma'ar da ta gabata sakamakon raunin da ta samu. Wanda akw zargin ya amsa laifinsa. Har ila yau, rundunar na cigaba da bincikar lamarin.

0 Response to "Yadda Yan Sanda Sun Cafke Dan Shekara 50 Da Ya Yi Wa 'Yar Shekara Uku Fyade Ta Rasu"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel