Test Footer

Abin Da Ya Sa Na Sha Gaban Duk Wani Furodusa A Kannywood – Sani SuleMasana’antar finafinai ta Kannywood ta haɗa mutane masu yawan gaske waɗanda idan ka bincika zaka ga kowanne da irin ta sa gudunmawar da yake bayarwa a wajen ci gaban harkar haka masana’antar ta faro tun farkon kafuwarta har zuwa wannan lokaci don haka duk inda ka duba a ɓangarorin sana’ar da take cikin harkar fim za ka tarar da wani jigo da ake ji da shi a wannan harkar. Furodusa Alhaji Sani Sule Katsina wanda aka fi sani da ‘Sani Real-Loɓe,’ wani jigo ne da a yanzu za a iya cewar ya tattara ɓangarori da dama na harkar fim da a yanzu shine ya ke riƙe da shi ta yadda ya zama wani jigo da a masana’antar samun kamar sa zai yi wahalar gaske. Domin kuwa a yanzu duk da irin yanayin da harkar fim take ciki na durƙushewa za a iya cewa shi Sani Sule ta harbi kasko saboda a wannan lokacin ne ya ke shafarinsa don haka ne ma kamfanin sa na Rite Time Multimedia ya zama wata kariya ga masana’antar Kannywood. Ba don komai ba sai don ganin cewar mafi yawan daga cikin kamfanin shirya finafinan sun daɗe ba a jin motsin su wasu ma tuni sun canza sana’a, amma shi Sani Sule Katsina ya tsaya tsayin daka don ganin masana’antar ba ta kai ga faɗuwa ƙasa ba don haka ne a yanzu ba dare ba rana kamfaninsa ya duƙufa wajen samar da finafinan masu inganci waɗanda suke ƙarawa masana’antar ƙima a idon duniya. Ko me ma ya jawo shi zuwa wannan masana’anta da kuma irin burin da yake da shi? Alhaji Sani ya ce, “Ita sana’ar fim sana’a ce mai kyau da za ka iya samun alheri a cikinta kuma ka bayar da gudunmawa ga al’umma ka faɗakar da su hanya da ba su sani ba, kuma ni a matsayina na furodusa. Shirya fim kawai nake yi na zuba kuɗina na yi fim, akwai finafinai da dama da na shirya irin su ‘Mafarki,’ ‘Ibro ya Auri Baturiya,’ ‘Matar Mutum Kabarinsa’ da sauran su, amma da yake yanzu yanayi ya canza musamman yanayin faɗuwar kasuwar fim. “Sai na koma harkar gidajen Talbijin nake shirya-shiryen na talabijin, don yanzu zan iya faɗa maka babu wani kamfani da yake shirya finafinai mai dogon zango wato series fim kamar kamfanina mai suna Rite Time Multimedia musamman idan ka na kallon shirye-shiryen Star Times ka san shirin da ake nunawa mai suna ‘Kukan Kurciya.’ To mu muka yi shi mun yi zango na ɗaya ana nuna shi yanzu daga an gama za a ci gaba da nuna kashi na biyu kuma ga wani babban fim shi ma da muka gama za a fara nuna shi nan gaba kaɗa mai suna ‘Sarauniya,’ don waɗannan ayyuka da muka yi ƙaramin furodusa ba zai iya yin sa ba. Ya ci gaba da cewa “Kasanc ita harkar fim mai dogon zango sai da kuɗi mai yawa, muna son harkar kasuwan amma dole muka barta, saboda taɓarɓarewar kasuwar da kuma masu satar fasaha, ka sanya kuɗi ka shirya fim ka gama ka kai shi kamfani a buga maka, kuma ka bada shi bashi a kasuwa, su ma su tura bashi, sai lokacin da aka ga dama za a baka kuɗin ka ga kuma masu satar fasaha suna daka mana wawa, a bin ma da suke yi mana ya fi ƙarfin kashi mu raba, sai dai mu kira shi kura da shan bugu gardi da karɓe kuɗi. “Can kuma kasuwa ba a sayar ba a maida maka da kayanka, don haka da muka ga duniyar ta canza wanda yana da wahala ka shiga gida goma ka samu huɗu da suke kallon DƁD sai dai tashoshin talabijin, don haka ne muka mayar da ƙarfin mu zuwa shirya finafinai masu dogon zango, duk da cewa akwai banbanci mai yawa a tsakaninsu saboda shi fim mai dogon zango yana ɗaukar dogon lokaci wanda za a iya shekara ɗaya, shi kuma wancan don gutsure ne za a gutsura maka idan ma labarin ya gamsar da kai ko bai gamsar ba za a gutsure labarin, amma shi mai dogon zango sai ka shekaa ɗaya kana kallo saboda cikakken labari ne ake ɗaukowa, ya kai inda ake so ya kai, tunda mu Hausawan mu sun raja’a ga sayane fim mai dogon zango na indiya sai muka ga me zai hana mu yi na Hausa yadda za su ƙaru da shi kuma ya maye na Indiya ɗin da suke kallo. “Kuma alhamdulillahi a yanzu zan iya cewa mun kama hanyar kaiwa ga nasara don kuwa ba cika baki ba ka je ka duba duk wani furodusa ka gani a yanzu za ka ga na sha gabansa ka je ofishin sa ka gani za ka haɗa shi da nawa don haka na sha gaban duk wani furodusa a Kannywood kuma ina godewa Allah da wannan matsayi da ya ba ni. Daga ƙarshe ya ce, “Irin yadda jama’a suka gamsu ma da aikin mu shi ma shaida ne don haka ƙungiyoyin matasa da ɗalibai da masu yiwa ƙasa hidima suke ƙarrma ni da lambar yabo musamman ƙungiyar matasan Arewa da ta ɗalibai ‘yan hidima. Sannan gashi a da taron da aka gudanar na bikin karrama ‘yan fim na City People a birnin Legas ni ne na zamo furodusa na farko sannan fim ɗin ‘Kukan Kurciya’ ya zamo na ɗaya a fim mai dogon zango da aka yi a wannan shekarar. Don haka muna roƙon Allah ya ƙara dafa mana a kan aniyarmu ta samarwa matasa aikin yi da kuma kyautata masana’antarmu ta Kannywood,” in ji shi.

0 Response to "Abin Da Ya Sa Na Sha Gaban Duk Wani Furodusa A Kannywood – Sani Sule"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel