Test Footer

Abin da zai faru idan Iran ta kai wa Saudiyya hariIdan kasashen Saudiyya da Iran suka fara yaki da junansu to hakan zai zama wani mummunan yaki da aka dade ba a ga irinsa, a cewar Paul Adams, wakilin BBC kan harkokin diflomasiyya. Sai dai ya ce babu wani mutum da yake ganin yaki zai iya barkewa tsakanin kasashen biyu, wadanda abokan gaba ne.
Amma ya ce kullum kasashen biyu suna nuna wa juna yatsa kuma suna yaki da juna ta bayan fage a wadansu kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.
Me ya sa Saudiyya da Iran suke zaman doya da manja?
Takaddamar da ke tsakanin Saudiyya da Iran a 'yan shekarun nan ta samo asali ne kimanin shekara 40 da suka wuce, daga yadda kowace take son samu gagarumin iko a yankin. Saudiyya wadda daga nan ne addinin Musulunci ya samo asali, tana ganin ita ya fi dacewa ta kasance jagoran kasashen Musulmin duniya. Sai dai a shekerar 1979 an samu juyin juya hali a kasar Iran, wanda Ayatollah Khomeini ya kafa gwamnati.
A lokacin ya samu tarbar lale marhabin daga gungun mutane wadanda ba a taba tara irin adadinsu ba a tarihin dan Adam. Daga nan ne kasar Saudiyya ta fara kallon kasar Iran a matsayin abokiyar gaba. Tun daga lokacin ne kuma fada a jin kasar Iran ya ci gaba da wanzuwa a yankin Gabar ta Tsakiya.
Saudiyya tana ganin barazana ne kasancewar Iran wadda take daga gabashinta da kuma Lebanon wadda ke yammacinta.
Hakazalika batun addini yana taka muhimmiyar rawa wajen ruruwar zaman tankiyar da ke tsakanin Saudiyya da Iran.
Don kowannensu yana wakiltar manyan bangarori biyu ne a addinin Musulunci, wato Saudiyya tana wakiltar Sunni, Iran kuma Shi'a .
Rashin jituwar da ke tsakaninsu yana da tushe daga wannan bambance-bambancen da ke tsakaninsu a addinance.
Ta yaya, kuma a ina ne suke yaki da juna? Adams ya ce a yakin kasar Yemen Saudiyya tana goyon bayan wani bangare, yayin da Iran take marawa daga gudan baya.
A kasar Syria, Iran tana tare da Shugaba Bashar al-Assad kuma tana tallafa mai da makamai da kuma dakaru. Saudiyya kuma tana taimakon 'yan tawayen kasar da kudi da kuma makamai.
Sai kuma Iraki, inda tun bayan karshen mulkin Saddam Hussein Iran take kara samun karfin fada a ji a can.
A Lebanon wadda wata kasa ce mai cike da tsarkakiya ta fuskar rabeben madafan iko, Iran tana mara wa kungiyar sa-kai ta 'yan Shi'a ta Hezbollah baya ne.
Hezbollah tana cikin gwamnatin kasar kuma tana da mayaka a Syria da Iraki da kuma Yemen.
Wannan ya sa Saudiyya take ganin ikon ya yi wa Iran yawa.
Mene ne abin yi?
Yarima mai jiran gado a masarautar Saudiyya, Muhammad ibn Salman, wanda shi ne yake tafiyar da kasar, ya fara matsa wa Iran lamba yana zargin cewa za ta karbe iko da kasashen Musulmi.
Mutane da dama suna tunanin cewa yariman ne ya umarci Firaministan Lebanon Sa'ad Hariri da ya yi murabus.
Firaministan ya bayyana murabus dinsa ne yayin da ke ziyara a Saudiyya a farkon watan nan.
"Ina so na shaida wa Iran da kawayanta cewa ba su yi nasara ba kan yadda suke shiga al'amuran kasashen Larabawa," in ji shi. Zargin da ake shi ne Saudiyya tana so ta fara yaki da Hezbollah ne, don ta rage mata karfin iko da kuma rage wa Iran iko.
Adams ya ce idan hakan ya tabba to babban abin tsoro ne don zai tada wani sabon yaki ne a yankin tsakanin Saudiyya da Iran.

0 Response to "Abin da zai faru idan Iran ta kai wa Saudiyya hari"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel