Test Footer

'Yadda aka tsaga gabana aka sa magani domin mallakar miji'. Wata matar aure wadda ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa Fatima Zahra Umar a shirin Adikon Zamani cewa, "ba ta taba samun ikon mallakar mijinta ba sai lokacin da ta je wurin wata mai maganin mata na gyaran gida ta tsaga mata gabanta tare da sanya magani a ciki." Ta ce "duk matan da suke cewa kayan mata ko kuma gyaran jiki karya ne to ba su san dawan garin ba ne kawai." Irin wannan batu na gyaran jiki ko kuma tsare gida da mata ke yi na janyo kace-nace a tsakanin magidanta har ma da malaman addini. Cikakkiyar hirar za ta zo muku ne a shirinmu na Adikon Zamani a ranakun Asabar da Lahadi da karfe 7:30 na safe agogon Najeriya da Niger.

0 Response to "'Yadda aka tsaga gabana aka sa magani domin mallakar miji'"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel