Test Footer

An kama mutane 4 bisa zargin yiwa uwar gidan shugaban kasa ihu a wajen taroAkalla mutane hudu ne aka garkame a kasar Zimbabwe sakamakon zargin su da jami'an tsaron kasar sukayi da laifin yi wa uwargidan shugaban kasar Grace Mugabe ihu a yayin wani taron gangamin da ta gudanar a satin da ya gabata.
To sai dai majiyar mu ta wata jaridar kasar mai suna Herald ta tabbatar mana da cewa tuni an saki mutanen a bisa kan beli kan laifin da ake tuhumar ta su.
NAIJ.com dai ta samu cewa siyasar kasar na dada kara daukar zafi musamman ma a tsakanin ya'yan jam'iyyar Zanu PF dake mulki inda yanzu haka ta rabe gida biyu ana ta takaddama a wajen wanda zai gaji shugaban kasar da yanzu haka yake da shekaru 93 a duniya.
Rahotannin da muke samu dai na nuni da cewa yanzu jam'iyya ta rabe gida biyu inda uwar gidan shugaban kasar ke jagorantar wani bangare yayin da kuma mataimakin shugaban kasar na jagorantar dayan bangaren.

0 Response to "An kama mutane 4 bisa zargin yiwa uwar gidan shugaban kasa ihu a wajen taro"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel