Test Footer

Ayyuka guda uku, ladan su ba ya shiga mizani a ranar alqiyamah saboda girmansuAyyuka guda uku, ladan su ba ya shiga mizani a ranar alqiyamah saboda girmansu:-
Daga Mal Ibrahim Daurawa
1. YIN AFUWA GA MUTANE:- Allah (SWT) ya na cewa, "DUK WANDA YA YI AFUWA KUMA YA KYAUTATA, TO LADANSA YA NA GA ALLAH"
2. HAKURI: Allah (SWT) bai fadi iyakar ladan da zai baiwa ma su hakuri ba. Sai dai ya ce:- "HAKIKA A NA BAIWA MA SU HAKURI LADANSU NE BA TARE DA LISSAFI BA"
3. AZUMI: Shi ma azumi Allah bai fadi ladan da zai baiwa ma su yinsa ba saboda girman sha'aninsa. Sai dai Manzon Allah (SAW) ya ce:-
"ALLAH (SWT) YA CE DUKKAN AYYUKAN 'DAN ADAM NA SA NE. AMMA BANDA AZUMI. SHI AZUMI NA WA NE, KUMA NI NE ZAN YI SAKAMAKO AKANSA". A ranar Alqiyamah wani mala'ika zai yi kira, ya na cewa:-
"INA MUTANEN NAN WADANDA LADANSU YA KE WAJEN ALLAH?!! Nan take sai ma su hakuri da ma su azumi da ma su afuwa su fito su ta fi wajen karbar sakamakonsu.

Ya Allah ka qara ma na hakuri da juna, da hakuri da qaddara, da kuma hakurin biyayyarka. Kuma ka sanya ma na taushin hali mu rika yafiya ga junanmu. Ka karba ma na azuminmu da dukkan ibadunmu.

0 Response to "Ayyuka guda uku, ladan su ba ya shiga mizani a ranar alqiyamah saboda girmansu"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel