Test Footer

Buhari ba shi da dalilin tsare Zakzaky – SoyinkaFarfesa Wole Soyinka ya ce ci gaba da tsare shugaban kungiyar 'yan Shi'a ta (IMN), Sheikh Ibrahim el-Zakzaky, ya keta haddin dan Adam. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da Jimeh Saleh , Editan sashen Hausa na BBC, yayin da ya kawo mana ziyara ofishinmu na Landan, kwanakin baya. Ya ce shi bai ga dalilin da ya sa za a ci gaba da tsare malamin ba, kuma "hakan kuskure ne." Kimanin shekara biyu ke nan da gwamnatin kasar take tsare da malamin bayan rikicin mambobin kungiyarsa da sojojin kasar a Zariya. Sai dai ya ce duk da cewa akwai fannoni da dama da gwamnatin Buhari "ta tafka kurakurai wadanda suka cancanci suka, akwai kuma fannonin da ya kamata a yaba mata". Ya ba da misali da yadda gwamnati ta yi aiki wajen gano kudin da aka sace wadanda aka kai kasashen ketare. Da kuma yadda aka sa "wadansu manyan jami'an gwamnati suka amayar da kudin da suka sace". Hakazalika farfesan ya ce shugaban zai iya cewa ya cika aikin da aka zabe wato aikin yaki da cin hanci da rashawa da kuma shawon kan rikicin Boko Haram da kuma makamantanta.

0 Response to "Buhari ba shi da dalilin tsare Zakzaky – Soyinka"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel