Test Footer

Cikakken Sharhi Akan mijin YarinyaTare Da:
Saddiƙa Habib Abba
Suna: Mijin Yarinya
Tsara Labari: Yakubu .M. Kumo
Furodusa: Nazir Auwal (Ɗan Hajiya)
Bada Umarni: Ali Gumzak
Kamfani: Ten Or Seɓen Entertainment
Jarumai: Aminu Sharif, Maryam Yahya, Sadiya Kabala, Bashir Na Yaya, Ado Gwanja, Mudansir Haladu, Ladidi Fagge, Yahanasu Sani, Asma’u Sani, Sani Garba S.K da Sauran su. Fim ɗin Mijin Yarinya labari ne na wani hamshaƙin mai kuɗi Alh. Ɗan Tani (Bashir Na Yaya) ‘ya’yansa biyu Raihana (Sadiya Kabala) da Bashir (Aminu Sharif) shi Bashir babarsa ta rasu ita kuma Raihana babar ta ba ta gidan sai matan Alhaji Dan Tani guda biyu da suke cikin gidan Lami (Asma’u Sani ) da Larai (Ladidi Fagge) amma kowaccensu bata ta Ɓa haihuwa ba.
wata rana Alhaji ya dawo gidan sa sai ya tarar da matansa Lami (Asma’u Sani) da Larai (Ladidi Fagge) su na yi da shi akan suna son ya mutu domin su sami dukiya, duk abunda suka samu na tumunin ta ka ba kowaccensu taci burin ta je ta sami saurayi ɗan shekara ashirin da biyar zuwa talatin ta aura ta more rayuwarta tunda Alhaji shi zaman hakuri kawai akeyi da shi babu abunda yake yi musu na soyyaya sakamakon tsufan da yayi. kuma su ba haihuwa su kayi da shi ba.
Alhaji Ɗan Tani yana jin wannan hirar tasu bai bari sun ga ne ya ji abunda suke faɗa ba amma tun a lokacin ya fara tinanin mai zai yi wanda zai dauki mataki akan matansa, kwatsam sai tunani ya faɗo masa akan ya je shima ya sami yarinya ƙarama ya aura ya more rayuwarsa kafin ya mutun tunda suma suna ƙi ƙi ra rin za su more ta su rayuwar idan ya mutu. ba da ɓata lokaci ba ya sanya direbansa Jibrin (Mudansir Haladu) ya samo masa yarinya karama wadda ba ta fi ce shekara sha biyar zuwa sha shi da ba, Jibrin ya kaishi gidansu Na’ima (Maryam Yahya) Alhaji Dan Tani ya yi wa Mahaifin Na’ima (Sani Garba S.K) bayanin abunda yake ta fe da su da farko mahafin Ni’ima ya fara ciwa Alhaji Dan Tani mutuncin shi bazai bashi ‘yarsa ba domin ya yi mata tsufa kuma shi tun tuni ya yi wa ‘yarsa miji A lokacin Alhaji Dan Tani ya siye shi da makudan kuɗi ta ke labari ya sha bam bam nan da nan ya amince da buƙatar Alhaji Dan Tani da farko ita ma Na’imar ta ki amincewa ta ce ya yi ma ta tsufa amma da ga karshe da mahaifiyarta (Yahanasu Sani) ta yi ma ta huduba akan ta yi hakuri ta aure shi tunda ya na da kudi nan da nan Na’ima ta amince za ta auri Alhaji.
A ɓangaran saurayin Na’ima Nazir (Shamsu Dan Iya) wanda da shi za ta aura har anyi musu baiko suna tsananin son juna shi da Na’ima tunda mahaifin Na’ima ya ki ra shi ya shai da ma sa cewar ya fa sa ba shi na’ima hankalinsa ya yi matuƙar ta shi har ta kai ga ya je gidan Alhaji Dan Tani tunda yaji labarin shi za’a baiwa Na’ima ya je ya nemi alfarma akan Alhaji yabar masa masoyiyar ta sa amma da ga karshe Alhaji sai ga shi ya si ye Nazir da kudi har da makullin mota da ga nan shi ma Nazir labari ya sha bam bam a gurin ya hakura bai kuma bi takan zancan na’ima ba.
Bayan Alhaji ya auri Na’ima Suka fara shan sha’aninsu na soyyaya ta re Alhaji ya zam to baya jin maganar kowa sai ta Na’ima duk abunda ta ke so shi za’ayi a gidan ragowar matan Alhaji su ka zama ba su da wani muhimmanci a idon Alhaji ya mai da su tamkar shara har sai da Bashir ɗan Alhaji ya da wo daga Jamani ya zo ya tarar da abunda ya ke faruwa a gidan shima suka fa ra ta kun sa ƙa shi da Na’ima ta fa ra yi ma sa rashin kunya duk san da ya yi yunkurin ra ma wa sai Na’ima ta ha da shi da mahaifinsa shi kuma ya kare masa ta tas a haka har Bashir ya hakura saboda biyyayar da ya ke yi wa mahaifinnasa ya ci ga ba da yi wa Na’ima biyayya yana bin duk abunda ta ce ashe lum lumbu ya yi mata sai daga karshe ya kulla mata makirci wata rana Alhaji ya sa ka shi ya kai ta unguwa a kan hanya ya kashe motar ya koma gidan ba ya kusa da Na’ima ya zauna ya nu na mata cewar shi fa tsakaninsa da Allah son ta ya ke yi tun lokacin da ya fa ra ganin ta saboda haka ta yarda kawai su dinga cin amanar Alhaji suna ficewa tare suna harkokin su tunda shi Alhaji duk bazai ma ta wannan ba tunda ta tsufa a haka a haka Bashir ya na ta ribatar Na’ima tun ba ta amince ba har ta zo ta amince da shi ta saki jikinta a motar ta na fadar Abunda ran ta yakeso akan Alhaji Har tana faɗin ita da ma wallahi ba son Alhaji ta ke yi ba kudinsa kawai ta ke so kuma ta yi kokarin tu sa soyyayarsa amma ta ka sa. duk wannan magan ganun da Na’ima ta ke yi ashe ba ta sa ni ba Bashir ya yi rukodin ne sai bayan sun ra bu akan sun ga ma amincewa juna Bashir ya je ya sami abokinsa ya kai ma sa rukodin ɗin ya ce ma sa ya sa ka ma sa acikin na ku ra mai kwakwalwa ya cire ma sa muryarsa ya bar ta Na’ima kawai sannan su ka sake ha da wani tuggun Bashir ya sa ke yin wa ta muryar da zummar ya na ba wa Na’ima hakuri akan bazai amince da buƙatar ta ba suka ha ɗa muryoyin guri gu da Bashir ya ka wo wa Alhaji ya ji a lokacin Alhaji ya kori Na’ima kuma ya sa ke ta suma matan na sa gu da biyun ya sa ke su tunda ya fuskanci duk ba don Allah su ke zaune da shi ba. Bashir da Raihana su ka ba shi shawarar ya da wo da mahaifiyar Raihana Alhaji Ɗan Tani kuma ya amince.
Abubuwan Birgewa:
1-Mai tsara labarin ya yi matuƙar ƙo ƙa ri saboda labarin kai tsa ye ya ta fi har ya di re bai kar ye ba sannan ya yi ƙo ƙa ri gurin san ya nishadi a ko wa na hoto na fim ɗin.
2- Jarumawan fim ɗin ko wannen su ya yi ƙo ƙa ri sosai wurin bai wa masu kallo nishadi da dariya a fim ɗin.
3- Hotunan fim ɗin sun fi ta tar tar hakan ya ƙayatar da ma su kallo.
4- Sauti ya fi ta raɗau a fim ɗin yan da ya ka ma ta.
5- Wuraran da akayi amfani da su a fim ɗin sun da ce da yana yin labarin.
Kurakurai:
1- A lokacin da Bashir (Aminu Sharif) ya shigo bayan mota ya zauna ku sa sosai da Na’ima ya na yin zaman da ya yi kusa- kusa sosai da Na’ima hakan ya saɓawa addinin musulinci domin ba maharraminta ba ne tunda an gina jaruman ne suna kan tafarkin addinin musulunci.
2- A yanda aka bayyana tarin dukiyar Alhaji Dan Tani a fim da irin manyan motocin da su ke gidansa da kuma yanda ya ke ji da Na’ima motar da Bashir ya kai Na’ima gidan biki sam bai ma da ce ace akwai irin wannan karamar motar ma a gidan Alhaji Ɗan Tani ba ballan ta na har a ɗauki Na’ima acikin wannan ƙaramar motar.
3- A lokacin da Na’ima ta buƙaci tana son shan alawa har ta aiki Bashir ya siyo ma ta a ƙofar gida acikin shago lokacin da Bashir ya siyo ya kawo ma ta alawar wannan ledar da aka sa ko alawar aciki leda ce irin wacce manyan kantina su ke amfani da ita amma ba shago irin na cikin unguwa kamar yanda Na’ima ta amba ta ba.
4- Acikin fim ɗin an nuna cewar Alhaji Ɗan Tani cikakken mutum ne mai hankali ba galma galma ba amma yanayin irin hirar da su keyi tare da mai gadin gidan sa Jalolo (Ado Gwanja) abun ya yi ya wa ace cikkakken mutum mai hankali ya na yin irin wannan surutan barkatai da irin wasu abubuwa da Alhaji ya din ga gudanar wa na soyyaya tare da Na’ima a gaban ‘ya’yan sa da direban sa da mai gadin sa cikakken mutum kamar Alhaji Ɗan Tani bai da ce a ganshi a wannan yanayin ba.
5- Alhaji Ɗan Tani An nuna shi a matsayin mutum mai tarin dukiya a fim ɗin amma har fim ɗin ya kare mai kallo bai ga sana’ar da ya ke yi ba, an dai ji wataran sau ɗaya ya faɗawa Na’ima yana da taro amma ba’a faɗi kona me ne ne ba, a irin wannan tarin dukiyarsa ya kamata ace an nuna sana’ar sa ko kuma an faɗe ta.
6- Acikin wasu hotuna na fim ɗin an dabar bar tar da hankalin wasu daga cikin masu kallo ba’a buɗe abun yanda kowa zai fahimta ba domin a wani hoto anji Alhaji yana maganar ƙan ƙa rar Na’ima kuma anji wataran suma iyalan Alhaji suna maganar ƙan ƙa rar har Bashir ya na cewa zai je ya ka she firji ƙan ƙa rar ta nar ke duk abunda za’ayi sai dai ayi a gidan, har su Lami da Larai suna bashi hakuri masu kallo da ya wa basu fahimci wannan hotunan na maganar ƙan ƙa ra ba shin ƙan ƙa rar ta meye ? tunda a yanda aka nuna tana da matuƙar muhimmanci.
7- A yan da aka nuna gidansu Na’ima da irin sutturar jikin Na’ima da iyayenta talaucinsu bai kai ace har lokacin da Alhaji Ɗan Tani ya bai wa mahaifin Na’ima dubu ɗari uku ba har ya din ga kuka yana Faɗar tunda ya ke a rayuwarsa ko dubu ashirin bai ta ɓa riƙewa a matsayin ta sa ba wannan gidan da aka nuna shi a matsayin gidansu Na’ima ko ha ya suke yi yafi ƙarfin ace wanda ya ka ma wannan gidan haya bai ta ɓa riƙe dubu ashirin ta sa ba.
8- An nuna yanda Naziru yake tsananin son Na’ima har yana faɗar cewa zai iya mutuwa idan bai sa me ta ba domin tun tana shekara shida ya ke rukon ta bai kama ta ace lokaci ɗaya da Alhaji ya buɗe masa ido da kuɗi ba akan yabar ma sa Na’ima ba ace Nazir ya yi saurin amincewa ya zaɓi kuɗin ya bar Na’ima ba a irin yanda aka nuna tsananin son da ya ke yiwa Na’ima da irin ko ke ko ken da ya ke yi akanta ace farat ɗaya ya ɗabi kudi akan soyyayar ta sa ba.
9- a hoton karshe na fim ɗin an nuna Alhaji da Bashir da Raihana a wani wuri a tsai tsaye ba’a bayyanawa mai kallo ina ne wannan wurin ba sannan magan ganun da suke tattaunawa muhimmancinsu bai da ce ace an nuna su suna yi akan hanya a tsai tsaye haka ba domin magana ce wadda ya kamata a gan su acikin gida a zaune ana tattauna ta.
Ƙarƙarewa
Fim ɗin Mijin Yarinya an yi mutuƙar ƙoƙari wurin nishaɗantarwa da abubuwan ba da dariya, amma wasu abubuwa da a ka nuna a fim ɗin a zahirance ba za su faru ba.
Allahu a’alamu.
Fimhausa

0 Response to "Cikakken Sharhi Akan mijin Yarinya "

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel