Test Footer

Dandalin Kannywood: Jaruma Nafisa Abdullahi ta samu kyauta ta 16 cikin shekaru 6 a LondonFitacciyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood mai suna Nafisa Abdullahi ta samu nasarar sake lashe wata gasa a karo na 16 acikin shekaru 6 da shafe a masa'antar shirya fina-finan kannywood a wani kayataccen biki da aka gudanar a birnin Landon.
Majiyar mu dai ta ruwaito cewa anyi gudanar da bukin bada kyautukar na African voice Newspaper da ta saba bayarwa duk shekara akan dukan yarukan yan Najeriya da kuma ya kan samu halartar manyan jarumai daga ko ina anyi shine a daren ranar Asabar din da ta gabata.
ta samu kuma dai cewa wadanda suka samu halarta bukin bayar da kyaututtukan dai akwai fitaccen jarumin nan Ali Nuhu, Ramadan Booth da kuma jaruma Nafisa Abdullahi da ma sauran su.
Da take tsokaci bayan karbar kyautar, jarumar ta godewa dukkan masoyan ta a bisa kwarin gwuiwar da suke bata a kowane lokaci sannan kuma ta sha alwashin ci gaba da kayatar da su.
Haka ma dai kwai kuma wadanda aka gayyata amma basu samu damar zuwa ba saboda dalilai daban-daban da suka hada da irin su Halima Atete da jaruma Hafsa Idris. ,

0 Response to "Dandalin Kannywood: Jaruma Nafisa Abdullahi ta samu kyauta ta 16 cikin shekaru 6 a London"

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel